Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun cafke wani bazawari mai suna Ariyibi Ahmed Olaseinde da wata mata da ta rabu da mijinta mai suna Akanbi Silifat Tunrayo, suna kan hanyar su ta zuwa ƙasa mai tsarki yin aikin Umrah
Jami’an na hukumar sun cafke mutanen biyu a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke a Ikeja jihar Legas, ɗauke da kilogiram 14.4 na hodar iblis d aka sanya cikin atamfa da leshe. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bamu Da Bukatar Kwankwaso a APC – Dan Bilki Kwamanda
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce an cafke Ariyibi ne a ranar Alhamis 20 ga watan Afirilun 2023, lokacin da ake tantance kayan shi a jirgin Qatar Airways mai tafiya daga Legas ta birnin Doha zuwa birnin Madina na ƙasar Saudiyya.
Babafemi ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa za a bashi la’adar N1.8m idan ya kai miyagun ƙwayoyin cikin nasara.
Haka kuma a ranar Laraba 19 ga watan Afirilu, jami’an hukumar ta NDLEA sun cafke wata mai suna Silifat Tunrayo Akanbi ɗauke da hodar iblis mai nauyin 2.90kg lokacin da ake duba kayan fasinjojin da ke a cikin jirgin Qatar Airways wanda zai ta shi daga Legas ya bi ta birnin Doha ya yada zango a birnin Jedda na ƙasar Saudiyya.
Babafemi ya ce duba jakunkunan ta da aka yi an samu ƙullin hodar iblis 6 mai nauyin 2.90kg da aka ɓoye a cikin atamfa.
Matawalle Ya Mayar Da Sarkin Yodoto, Bayan Dakatar Da Shi Tsawon Watanni
Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da Alhaji Aliyu Garba Marafa a matsayin Sarkin Birnin Yandoto.
A watan Yulin shekarar da ta gabata, Matawalle ya dakatar da sarkin saboda ya ba wani sarkin ‘yan fashi, Ado Aleiru mukamin sarauta.