Hukumar tsaron fararan hulda da kaddarorin Gwamnati NSCDC reshen jihar Zamfara, ta ce jami’anta sun kama wani ma’aikacin POS mai suna Mustapha bisa zargin yin hada-hadar kudi ga ‘yan bindiga. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kwamandan hukumar dake jihar, Muhammad Bello Muazu ne ya bayyana haka , a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce an kama mai laifin ne a yayin da yake yin wannan harkarlar a yankin Birnin Tsaba da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Diri Ya Rantsar Da Mukaddashiyar Alkalin Alkalai
Ya cigaba da cewa, ‘Jiami’an sun kwato injinan POS guda biyu, inda ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa wani shugaban ‘yan fashi ne ya saya masa injinan.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa cewa yana amfani da na’urar POS ne kawai wajen yin kasuwanci a madadin ‘yan fashin.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya shaida wa majiyar Dimokiradiyya cewa sun buga masa waya daga dajin inda suka umarce shi da ya karbi kudi a madadinsu ya ajiye kudin a wurinsa.” Yace
A cewarsa, idan ‘yan fashi suna son siyan magunguna, man fetur ko kayan abinci, sai su tura wani kai tsaye wurin wanda ake zargin ya karbi kudin ya saya musu duk abin da suke so.
“Bisa lira da muka yi, hakan zai shafi yadda ‘yan fashin ke amfani da POS na karkara wajen hada-hadar kasuwanci. Ma’aikatan POS na karkara sun fi kusa da masu aikata laifuka,” ya bayyana.
A wani labari kuma, Za Mu Doke Manchester United A Filin Wasa Na Emerates — Dan Wasan Arsenal Ya Ci Alwashi
Dan wasan baya na Arsenal William Saliba ya ce Gunners din za ta doke Manchester United idan kungiyoyin biyu za su kara a gasar Premier a karshen mako. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Manchester United ta sha kashi a hannun Arsenal a karawarsu ta farko a gasar Premier bana, bayan da ta doke Gunners da ci 3-1 a Old Trafford.
Comments 1