Gwamnatin Tarayya ta ce, akalla ma’aikatan lafiya 40 suka harbu da cutar Korona a yayin gudanar da ayyukansu, abin da ke dada fito da hatsarin da ke tattare da mu’amala da masu dauke da cutar.
Ministan lafiyar kasar, Osagie Ehanire ya sanar da haka a jawabin da ya saba yi wa al’ummar kasar a kowacce rana dangane da matakan da gwamnati ke dauka wajen yaki da wannan cuta.
Ehanire ya gargadi ma’aikatan lafiya da su rika daukar matakan kariya a daidai lokacin da suke kokarin ceto rayukan masu dauke da cutar, yayin da ya sanar da killace wasu karin jami’an kula da lafiyar.
Rahotanni sun ce, a kalla asibiti masu zaman kansu guda 17 a Legas suka sanar da cewar wasu ma’aikatansu sun yi mu’amala da masu dauke da cutar, abin da ya sa gwamnati ta dakatar da ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Gwamnatin Tarayya ta bukaci asibiti masu zaman kansu da ke bukatar kula da masu fama da cutar COVID-19 da su yi rajista kafin fara aikin, a daidai lokacin da cutar ta kama mutane 873, kuma 28 daga cikin su sun mutu, yayin da 197 suka warke kamar yadda Rfi Hausa suka tabbatar.