An kalubalanci hafsoshin rundinar Sojojin Najeriya da suka kammala karban horo daga kwalejin dabarun yaki ta kasa da su yi amfani da Ilimin da suka samu ta hanyar da ta dace wurin inganta aiyukansu na samar da tsaro a kasa.
Kwamandan kwalejin, Manjo Janar Charles Ofoshe ne ya yi wannan kira a lokacin bikin yaye hafsoshin guda 66 a Abuja.
Ofoshe wanda ya bayya kwarin gwiwa kan kwarewar da jami’an suka samu, ya ce duba da irin ingantaccen horo da kwalejin ke bayarwa, ya na da tabbacin jami’an za su iya magance barazanar rashin tsaro a Najeriya.
A cewarsa, “An tsara kwasa-kwasan da aka koyar da jami’an Sojin ne don shayar da su ilimin da dabaru ta yadda za su kware su yi aiki yadda ya kamata a matakan aikin soja da makamancin haka.”
Shugaban kwalejin ya yaba wa babban hafsan rundinar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai bisa goyon baya da samar da ci gaban ababen more rayuwa a kwalejin.
Ya bayyana ce Janar Buratai ya ba da wani katafaren gini don tabbatar da cewa mahalarta kwalejin sun ci gaba da samun horo cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Shima da yake jawabi a wurin bikin, Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi (mai ritaya) kuma babban bako a bikin ya kalubalanci jami’an da su kasance jagorori na kwarai a duk inda suke.
Magashi ya kara da cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da tallafawa kwalejin da dabarun jagoranci mai ma’ana da ma sauran abubuwan da ake bukata na gudanar da kwalejin.