An girke Jami’an tsaro bila adadin a unguwar Ama Awusa dake birnin Owerri na Jihar Imo don baiwa al’ummar hausawa mazauna gurin cikakken tsaro.
Wannan Mataki ya biyo karuwar yawaitar kai hare hare ne da ake yi yan arewa mazauna kudancin kasar nan.
A makon da ya gabata kawai an kashe yan tireda bakwai a kauyen Orlu dake yankin Umuaka na karamar hukumar Najba dake jihar ta Imo.
A yau Juma’a ne Babban Mai tallafa wa gwamnan Jihar Kan Jinsi da Mutane Masuu nakasa Suleiman Ibrahim Suleiman ya tabbatar da labarin girke jami’an tsaron don kare ci gaba da aukuwar hare haren.
Ya Kuma shawarci Yan Arewa dake kokarin ganin sun aikata makamancin abinda ke faruwa a yankin kudu kan yan kudu mazauna arewa da su shafawa kan su ruwa, domin a cewar yan siyasa marasa kishin zaman lafiya ne ke yunkurin cimma muradan su.