Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ta kori dukkanin ma’aikatanta da ta dauka wadanda suke bakunci a jami’ar da kuma wadanda suke aiki a matsayin Kwantiragi a jami’ar.
Sanarwar dakatarwa na dauke da sa hannun Mrs Ramatu Muhammad a madadin Magatakadar Jami’ar A. A Kundila, wacce aka rubuta a ranar 11 ga watan Yunin 2020, kuma aka aikawa da shugaban Jami’ar, mataimakin shugaban Jami’ar a bangaren mulki, da kuma sashen ilmi, da kuma mai binciken kudin kwakwaf na Jami’ar, da kuma shugaban dakin karatu na jami’ar.
Sanarwar ta bayyana cewa; daga ranar 15 ga watan Yunin 2020, hukumar gudanarwa ta jami’ar tana bakin cikin sanar da dukkanin ma’aikatan da suke kan Kwantiragi, ko masu bakunci, da kuma masu mukaman wata-wata da cewa an soke wannan damar da aka ba su ta aiki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; “An bada damar kwana Talatin mutum ya shirya barin jami’ar daga 15 ga Yunin 2020, zamu kuma raba wa ma’aikatan da wannan kora ya shafa shaidar korarsu.”
Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayanin ko mene ne dalilan wadannan Koran ba.