By Ishaq Dabai
Jami’ar Bayero Kano ta tsawaita ranar dawowa makaranta dan cigaba da zangon karatu na 2021/2022 zuwa 1 gawatan Nuwamba 2021.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa majalisar dattijai ta jami’ar a taronta na 392 data gudanar a ranar Laraba, tace ta amince da sabuwar ranar komawa aiki.
Sanarwar da Sakataren yada labarai na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar ga mukaddashin magatakardar jami’ar, Malam Jamil Ahmed Salim yace shawarar sake tsawaita ranar dawo aikin ita ce dan ta samu ta karbi wadanda suke son shiga jami’ar Wanda har yanzu ba a fitar da sakamakon SSCE na 2021 ba.
Sanarwar dangane da cewa za a fitar da sakamakon jarabawar NECO a hukumance a makon farko na watan Oktoba dan fatan baiwa masu neman samun gurbin karatu a jami’ar damar cancantar shiga jarabawar, Majalisar Dattawa itace ta yanke shawarar tsawaita ranar sake dawowa da wata daya. domin karbar dalibai da dama don rage yawan faduwa.”
A cewar sanarwar, sabon zangon karatun na 2021/2022 yanzu zai fara aiki daga ranar 1 ga Nuwamba, 2021, yayin da za’a fara gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2021.