Sakamakon zaben Shugaban kasar Zambia a yau Litinin, ya nuna cewa, jagoran Yan adawa a kasar Hakainde Hichilema ne ke kan gaba da tazara mai yawan gaske, kan abokin hamaryan shi wato Edgar Lungu.
Hukumar zaben kasar ta ce, Hichilema ya samu kuri’u 2,810,777, ya yin da Lungu ya samu 1,814,201, daga cikin kuri’un da aka kada, bayan an kammala kirga dukkannin mazabu 156 dake kasar.
A wurin tattara sakamakon zaben dake Lusaka babban birnin kasar, Shugaban hukumar zaben Esau Chulu ya ce, ” Ina sanar da al’uma cewa, Hachilema ne ya lashe zaben Shugaban kasar Zambia” a cewar shi.
Kazalika hakan na nuna cewa, wannan shi ne karo na uku, da Shugaban cin kasar ke sauya sheka daga hannun jam’iya Mai Mulk,i zuwa Jam’iyar hamaiya, tun bayan samun yancin kan kasar a shekarar 1964 daga Kasar Burtaniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kashe Mutum 3 a wani sabon hari a Kudancin Kaduna
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito yadda magoya bayan Hichilema a daukacin fadin kasar, suka fara murnar nasarar lashe zaben na shi. Inda su ka fito sanye da tufafi Mai launin Ja, da ruwan kwai, domin nuna goyan bayan su ga jam’iyar UPND. Ya yin da su ke ci gaba da raye-rayen da wake-wake a kan Tituna.
Hichilema Mai shekaru 59 a Duniya, ya rike Shugaban wata kamfanin, kafin shigar shi siyasa, Wanda ya ke fatan zai cire wa kasar kitse a wuta, na matsin tattalin arziki da kasar ke ciki.
Sai dai Kuma agefe guda, Lungu Mai shekara 64, haryanzu bai amince da kayan da ya sha ba a zaben, Wanda ake ganin cewa, zai iya kalubalantar sakamakon zaben.
Kazalika idan za’a iya tuna, ko a ranar Asabar din da ta gabata, Lungu ya zargi cewa, ” Zaben ba sahihi ba ne” bayan wani ya mutsi ya barke lokacin da ake tsaka da kada kuri’a, a mazamu uku dake kasar.
Sai dai tuni manyan masu fada aji a jam’iyar UPND, su ka yi watsi da ikirarin da Lungu ya yi.