Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan abin da ta bayyana a matsayin kisan kare dangi a jihar Filato.
Jam’iyyar PDP ta zargi Tinubu da kasa ziyartar al’ummar Filato da abin ya shafa, inda ta kara da cewa rashin jajircewar shugaban kasar ba zai haifar da da mai ido ba.
Karanta nanGwamnan Jahar Katsina Ya Dakatar Da Jami’in Gwamnati Akan Badakalar Fili
Babbar jam’iyyar adawa ta kuma dage kan binciken kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, binciken ICC kan kisan kiyashin.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa a jajibirin Kirsimeti, an kashe sama da mutum dari a wasu garuruwa sama da 20 na jihar Filato,inda dama suka jikkata, gidaje da ababen more rayuwa sun ruguza sakamakon aukuwar lamarin a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar.
Jam’iyyar PDP ta caccaki Tinubu kan abin da ta kira gazawarsa wajen ziyartar wurin da ‘yan ta’adda suka yi wa ‘yan Nijeriya kisan kiyashi a jajibirin Kirsimeti a yankunan Bokkos da Barkin Ladi na Jihar Filato.
Jam’iyyarmu ta tabbatar da cewa gazawar Shugaba Tinubu wajen nuna tausayawa ga al’ummar Filato babban abin damuwa ne inji wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran PDP Debo Ologunagba.
A wani labarin kumaLebura Zai Shafe Watanni 5 A Gidan Yari Bayan Satar Fitulun Kan Titi
Jam’iyyar PDP ta damu matuka yayin da ‘yan Najeriya ke tambayoyi masu daure kai kan abin da ya haddasa gazawar bayanan sirri kafin da kuma lokacin kisan gillar da aka shafe sama da sa’o’i 48 ana yi.
Don haka dole ne shugaba Tinubu ya kawar da fargaba da damuwa kan abubuwan da ke faruwa ta hanyar kai ziyara ga al’ummar da abin ya shafa cikin gaggawa tare da yin jawabi ga al’ummar kasar kan sahihan matakai na gano wadanda suka aikata wannan aika-aika da masu daukar nauyinsu.