A ranar Juma’a ne wata kotu dake Dei-Dei da ke Abuja ta yanke wa wani ma’aikaci mai suna Aminu Shuaibu mai shekaru 37 hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin satar fitulun kan Titi.
Kotu ta yanke wa Shuaibu da ke zaune a unguwar Gauraka a Jihar Neja hukunci bayan ya amsa laifin sata da ake tuhumarshi da ita.
Karanta nanZamfara: Kaddarorin Naira Miliyan 273 Sun Lalace a Shekarar 2023 – Hukumar Kashe Gobara
Sai dai alkalin kotun, Aliyu Kagarko, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar Naira 20,000.
Alkalin kotun ya gargadi wanda aka yankewa hukuncin da ya kasance mai halin kirki kuma ya daina aikata laifuka bayan ya kammala zaman gidan yari.
Ya ce hukuncin zai yi tsauri idan wanda aka yanke wa hukuncin bai ceci kotun ba daga tsawaita zaman shari’a.
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Stanley Nwaforaku, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Ibrahim Lawal na Civilian Joint Task Force (CJTF) titin filin jirgin sama na Gosa Toge, Abuja ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Iddo a ranar 9 ga watan Disamba.
A wani labarin kumaGwamnan Adamawa, Fintiri Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 Na N225.8bn
Nwaforaku ya ce a wannan rana da misalin karfe 4:20 na safe, wanda aka yankewa laifin ya saci wata igiyar fitilar titi amma wanda ya shigar da karar ya kama shi yana aiki a Gosa Toge.
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa, a yayin da ‘yan sanda suke gudanar da bincike wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa, inda ya kara da cewa laifin ya ci karo da sashe na 288 na kundin laifuffuka.