By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar APC reshen jihar Borno ta rantsar da shugabannin kananan hukumomi da mambobin kwamitin ayyuka na jihar gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa da za a yi ranar Asabar.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Ebonyi Ta Musanta Zargin Cin Hancin Da Ake Yiwa Umahi
An rantsar da shugabannin kananan hukumomi, masu zartarwa na jiha, da wakilan jihar domin gudanar da babban taron da za a yi ta hannun shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Maiduguri, Muhammad Umaru Esq.
Rantsarwar wadda ta gudana a dakin taro na Sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri ta samu halartar shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Borno Farfesa Isa Marte da shugaban jam’iyyar Ali Dalori da sauran ‘yan majalisar zartarwa na jihar.
Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da shugaban jam’iyyar Ali Dalori wanda ya zama shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar APC ya ce jihar Borno har yanzu ba ta dauki wani dan takarar shugaban Jam’iyyar ba a tsakanin ‘yan takara uku.
“A matsayina na shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar APC, ina mai tabbatar maka da cewa jam’iyyar na kokarin ganin an gudanar da babban taronta cikin nasara kuma dukkanmu mun amince a matsayinmu na shugabannin jam’iyyar a Jihohinmu daban-daban cewa duk abin da Shugaba Buhari ya ce shi ne zamu yi. Idan shugaban kasa ya nada daya daga cikin masu neman takara uku, shi ne wanda za mu amince da shi. cewar Dalori.
Ya ci gaba da bayyana cewa Borno ta samu amincewar sauran jihohin Arewa goma sha takwas don samar da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa ta Arewa a gaban sauran masu neman takara.
“Mu a Borno muna da hurumin dukkan jihohin Arewa goma sha tara mu samar da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a Arewa na jam’iyyar duk da cewa akwai sauran masu neman takara daga wasu Jihohin. Ali Dalori ya kara da cewa.
Kwamitin ayyuka na jihar da aka kaddamar ya hada da shugabannin mata na shiyya uku masu wakiltar Borno ta tsakiya, arewa, da Borno ta kudu da kuma shugabannin matasan shiyyar na shiyyoyin Sanatoci uku.