Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyarsa za ta kawo karshen kalubalen tsaron da ke addabar Najeriya idan har aka zabe ta karbi ragamar shugabancin kasar a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ya yi wannan alkawarin ne a wata tattaunawa da wasu zababbun ‘yan jarida a Sokoto inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar Labour za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
KARANTA KUMA: Kwankwaso: Jam’iyyar Labour Ba Za Ta Iya Lashe Zaben 2023
Ya ce jam’iyyarsa za ta dogara ne kan fasahar kere-kere tare da hada hannu da masu ruwa da tsaki don ganin an kare kowace murabba’in mita a cikin yankin Najeriya tare da dakile hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami.
Baba-Ahmed ya kuma yi alkawarin cewa jam’iyyarsa za ta juya tattalin arzikin kasa tare da kare hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsare da sakamakon gogewa da masaniyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi kan harkokin tattalin arziki.
Gidan talabijin na Channels ta rawaito cewa, Baba-Ahmed ya ce rikicin da ke kunno kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Ma’aikatan Jami’a, za a magance shi ne a lokacin da Jam’iyyar Labour ta karbi ragamar mulkin kasar nan, domin kuwa ilimi za a bai wa fifiko a gwamnatinsu.
A wani labarin kuma: Tinubu Ba Ya Bukatar Ya Nuna Wata Hujja ta Rayuwa – Umahi
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana da rai kuma baya bukatar ya nuna wata hujjar rayuwa.
Asiwaju yana da rai kuma ba ya bukatar ya nuna wata hujja ta rayuwa kuma kuna iya ganin hakan, “in ji Umahi a cikin shirin Sunrise Daily na tashar talabijin ta Channels a ranar Litinin din nan.