Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Yobe, tayi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar wanda hunumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana.
Jami’in sanya ido kan tattara sakamakon zaɓen na jam’iyyar, Ibrahim Garba Muhammad, shine ya bayyana hakan.
KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin da APC da PDP suka lashe zaɓen gwamna ya zuwa yanzu
Da yammacin yau Lahadi 19 ga watan Maris 2023 ne ya bayyanawa manema Labarai cewa, Jam’iyyar NNPP bata amince da sakamakon zaben Gwamna da ‘Yan Majalisu a Jihar Yobe ba.
“Muna da manyan hujjoji, wadan da suka tabbatar mana cewa Jam’iyyar APC ta tafka magudi a rumfuna da dama a fadin kananan hukumomin Jihar Yobe”, inji Ibrahim Garba Muhammad.
Yace wasu daga cikin hujjojin da suke da su sun hada da sayan kuri’u a rumfunan zabe ta hanyar baiwa mutane kudi a tilasta musu jefawa APC, yin kamfe a ranar zabe, rarraba kyaututtuka ga masu zabe kamar kayan abinci, da atamfa da sauransu.
Bayan haka kuma, ya bayyana cewa an yi barazana ga masu zabe ta hanyar nuna musu cewa idan basu zabi jami’iyyar APC ba, zasu fuskanci matsala da kuma kada kuri’u fiye da abun da aka tantance.
Ibrahim Garba Muhammad yace NNPP zata je Kotu domin neman ƙalubalantar sakamakon zaɓen.