By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP ta yi kira da a kori Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Timipre Sylva kan shigo da gurbataccen man fetur mai guba da kuma rarraba shi a fadin kasar.
Jam’iyyar ta zargi Ministan da yaudarar ‘yan Najeriya tare da boye wasu muhimman bayanai kan man mai guba a matakin farko.
A cewar PDP, Sylva ya gaza wajen gudanar da ayyukansa na jama’a ta hanyar kin bayyana sunayen wadanda ke da hannu a badakalar.
An yi wannan kiran ne biyo bayan bukatar da hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa (NNPC) ta yi na neman Naira biliyan 201 domin tsaftace gurbataccen man.
Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Laraba, ya zargi gwamnatin APC da yin sama da fadi da dukiyar kasa tare da shigo da man mai guba da gangan tare da neman Naira biliyan 201 domin a tsaftace tabarbarewar.
A cewar jam’iyyar PDP, abin kunya ne ga gwamnati ta kara zare kudi daga asusun kasa ta hanyar neman zana wadannan kudaden.
Jam’iyyar adawar ta dage cewa a gano wadanda ke da alhakin shigo da man a kuma sanya su su dauki nauyin tsaftace muhalli.
Jam’iyyar ta ja kunnen gwamnati kan kara matsawa ‘yan Najeriya su fito kan tituna domin nuna adawarsu.
PDP ta zargi gwamnatin da girman kai, cin hanci da rashawa da kuma rashin sanin yakamata, PDP ta ce akwai makarkashiya don kare wadanda suka aikata wannan badakala.
Jam’iyyar ta bayyana cewa badakalar ta jefa al’ummar kasar a kan gaba, ta ce hanya daya tilo da za ta iya kawar da wannan tada zaune tsaye ita ce gwamnati ta bankado masu hannu a cikin badakalar.
Ta dage cewa dole ne a sanya masu laifin su biya diyya, musamman ga wadanda gurbataccen man fetur ya lalata ababen hawansu da kayan aikinsu tare da daukar nauyin wannan tsaftar.
Jam’iyyar PDP ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mika ma’aikatar man fetur da kuma baiwa kwararrun damar rike ma’aikatar domin dawo da hayyacinta a kan tsarin.