Kungiyar ASUU reshen Jami’ar Bayero, Kano. Sun amince da Tsunduma Yajin Aikin gargadi, na sati hudu domin marawa uwar kungiyar ta Kasa baya wajen garkame Jami’o’in.
Cimma wannan matsayar ta faru ne a yau, bayan kammala tattaunawa tsakanin Kungiyar Daliban Jami’ar da kuma Kungiyar ASUU reshen Jami’ar.
Yanzu Haka dai sanarwar ta tabbatar da cewa daga yau, an dakatar da duk wata harkar jarrabawa tsakanin Daliban Jami’ar.
A karshe sanarwar Mai dauke da sa hannun Kwamared Aminu Murtala Yahaya Mai magana da yawun kungiyar daliban, ta bukaci iyaye su ci gaba da hakuri da kuma addua Kan halin da ‘Ya’yansu suka shiga na zaman gida.