Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP a jihar Osun ta baiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode wa’adin sa’o’i 24 da ya yi wa jama’a bayanin dalilin da ya sa ta kama mambobinta da tsare su ba bisa ka’ida ba.
Wata sanarwa da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar, Akindele Adekunle, ya fitar a ranar Asabar, ta ce jam’iyyar ta bukaci ‘yan sanda su yi wa jama’a bayani kan dalilan da suka sanya suka fara kame dimbin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a wadannan ‘yan kwanakin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zaben-ekiti-inec-ta-yi-kira-da-a-gaggauta-hukunta-masu-siyan-kuriu-da-aka-kama/
Adekunle ya zargi Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na Jihar Osun, Remi Omowaye da kai jami’an ‘yan sanda zuwa gidajen ‘yan jam’iyyar PDP a wasu kananan hukumomin jihar domin kama su da karfi ba tare da dalili ba.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kai farmaki gidajen ‘yan jam’iyyar PDP a Ijebu-Ijesa da Eti Oni a kananan hukumomin Oriade da Atakumosa ta Gabas.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa ‘yan sanda suna gudanar da kamen a cikin dare, “harbin bindiga na lokaci-lokaci, wanda hakan ya sanya wadanda abin ya shafa da ‘yan uwansu suka gamu da rudani.
“Wannan shine kololuwar cin zarafi da dan majalisar ministocin gwamnatin Gboyega Oyetola ke yi da kuma rashin da’a a bangaren ‘yan sanda saboda ba da kansu ga cin zarafin ‘yan kasa da ake biyansu ba bisa ka’ida ba.
PDP ta kuma zargi jami’an kungiyar tsaro ta Kudu maso Yamma mai suna Amotekun da zama wani makami na musgunawa al’ummar jihar saboda a cewar sa sun sabawa manufar farko da aka kafa ta.