Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana hangen nesa ga shugaba, jajirtacciyar al’umma, da kuma aiki da lokaci, a matsayin ginshikan farfadowa daga tashe-tashen hankula.
Gwamna Buni ya bayyana hakan ne jiya Litinin, lokacin da Jakadan kasar Japan a Nigeria, Mr. Matsuyama Kazuyoshi ya kai masa ziyarar gaisuwa a fadar gwamnatin jihar.
Gwamna Buni yace darrusan da ya koyo yayin ziyarar da ya kai Birnin Hiroshima, na kasar Japan, zasu taimaka matuka wajen farfado da wuraren da tashe-tashen hankulan Boko Haram ya tarwatsa na tsawon fiye da shekaru goma a fadin jihar.
“Duk da yanayin ya banbanta, amma hanya mai bullewa itace shugabanci mai tafiya bisa hangen nesa hadi da jajircewar al’umma da kuma aiki da lokaci wajen kawo sauyi bayan tashe-tashen hankula”.
“Shugabanci da hange, da kuma jajircewar al’ummar da iftila’i ya shafa, sun zamo abin koyi garemu wajen cimma maradan mu”, inji Mai Mala Buni.
A cewar Gwamnan, Gwamnatin Yobe zata yi amfani da irin salon birnin Hiroshima wajen Farfaɗo da wasu daga cikin abubuwan da masu tada kayar baya suka lalata.
Gwamna Buni yace, ilimi, kiwon lafiya, karfafa hanyar dogaro da kai da kuma samar da ayyukan yi sune bangarorin da suka dace a baiwa fifiko cikin kokarin da ake yi na neman farfadowa daga tashe-tashen hankula, yana mai nuna bukatar tallafi da hadin kai daga Gwamnatin Japan.
Tun da fari, a nasa sa, Jakadan na Japan a Nigeria, Mr. Matsunaya ya nemi hadin kai daga Gwamnatin Yobe.
Ya kuma yi alkawarin cewa Gomnatin Japan a shirye take wajen samar da ayyukan yi ga ‘yan jihar Yobe ta hanyar noman waken suya.
Har ila yau, yace Gwamnatin Japan zata taimakawa jihar Yobe da wadatuwar abinci tare da inganta tsarin noman rani a jihar.