An samu fashewar Wani abu a sansani sojijn dake Crimea yankin da Rasha ta mamaye, wanda yayi sanadiyar jikkata mutum biyu.
Jami’an Rasha sunce wuta ta ta shi a a wurin ajiye makamai na Dzhankoi a arewacin Crimea.
Haka kuma ana iya ganin wutar a karamar tsahar wutar lantarki yankin.
Sai dai ba san mussabbain tashin wutar ba , ko da yake a makon da ya gabata an ga jami’an Ukraine sun kaiwa jiragen yaƙin Rasha hari a gaɓar iyakar yankin na Crimea.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai bada mashara a ofishin shugaban kasa Ukraine Mykhailo Podolyak yace an kai wannan farmakin ne domin rage yawan sojojin.
Shugaban yankin Crimea Refat Chubarov ya bayyana cewa ana iya jin karar fashewar wani abu, a wurin mai nisa.
Ma’aikatar tsaron Rasha tace wutar ta tashi ne a wurin ajiye makamai na wucin gadi da ke kusa da garin Maiske da misalin ƙarfe 6:15 a gogon Mascow, wanda yayi dai dai da 3 15 agogon GMT, kuma ana ci gaba da gudanar da binciken mussabbin tashin wutar.
An kuma tabbatar cewa, hanyar jirgin kasa ta tsaya cak Saboda matsalar da ta samu.
Ma’aikatar tace ba’a samu wadanda suka samu rauni sosai ba , amma shugaban yankin da Rasha ta nada Sergie Aksyonov ya ziyarci wurin , inda yace tunkan faruwar lamarin, sun kwashe mutane dubu biyu 200 zuwa wani gari mafi kusa, kuma mutum biyu ne kacal suka samu rauni sanadiyar farmakin.
A shekarar 2014 ne Rasha ta kwace yankin Crimea daga hannun gwamnatin Ukraine, haka kuma a lokacin da dakarun Rasha suka kaddamar da sabon yaƙi a Ukraine cikin watan Febuwairu suna amfani da wurin a matsayin sansani sojin, domin kwace manyan garuruwa a kudancin Ukraine.
Rasha dai ta mamaye yankuna biyu na kudanci musamman Kherson da Zaporizhzhia, Sai dai kuma Ukraine ta lashi takobin kaddamar da farmaki domin kwato yankunan da ke karkashin ikon Rasha.
Bayanai daga ma’aikatar tsaron kasar Ukraine sun tabbatar da cewa sojojin kasar sun yi amfani da makaman Himars kirar Amurka wurin kaddamar da hare hare a wuraren ajiye makamai 50 mallakin Rasha.
Haka kuma an tabbatar da cewa lamarin ya shafi gadoji a kudancin kasar , wanda ya shafi hanyoyin da ke kai kayayyakin daga Crimea zuwa Kherson.
Duk da haka, a iya cewa kokarin da sojojin Ukraine ke nunawa wurin isa ga abokan gaba, zai shafi dakarun Rasha kwarai da gaske.