Rundunar Sojin Nigeria dake Kaduna ta samu nasarar ceto mutane goma da aka yi garkuwa da su a rukunin gidajen Ma’aikatan Jiragen sama na Kaduna ba tare da ko kwarzani ba.
Rundunar ta ce wannan nasara da ta samu a ranar Larabar da ta gabata ya biyo bayan wani samame ne da ta gudanar a wani katafaren gandun daji na jihar inda suka yi ido biyu da masu garkuwan.
Rundunar ta kara da cewa masu garkuwan sun bude wa sojin wuta yayin da suka yi ido biyu da su, to saidai yayin su mma sojin suka fara musayar wuta daga bisani sun yi galaba a kan masu garkuwa da mutanen inda suka arce suka bar mutanen.
Tuni kuma aka kwashe wadannan mutane goma wanda suka hada da namiji guda, mata uku da kuma yara kanana guda shida inda aka kai su asibitin soji don ci gaba da basu kulawa ta lafiya.
A wani lamari na zuwa da kai da aka ce ya fi sako, Gwamnan jihar ta Kaduna Mallam NAsir el-Rufa’i ya jinjina wa rundunar sojin bisa wannan namijin kokari inda ya isar da juayin shi ga wadanda suyka tsallake rijiya da bayan.
Da yake tofa albarkacin bakin shi Kwamandan runudan ta daya ta jihar Kaduna Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi ya jinjina wa rundunar bisa jajircewar su inda ya tabbatar da alwashin Hafsan Sojin Najeriya na cewa ana gabda shafe ayyukan yan fashin daji a duk fadin kasar na.
Idan za a iya tunawa dai an yi garkuwa da mutanen ne a ranar shida ga watan Maris din shekarar da muke ciki yayin da yan bindigar suka kutsa rukunin gidajen ma’aikatan filin jirgin saman.