Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun kama wata sai da Maganin gargajiya da wasu mutane biyu da suka kware wajen bangani gawarwaki a cikin kabari a jihar Edo.
Rahotanni na nuna cewa ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Mayun wannan shekarar
Wadanda ake zargin sun hada da: , Josephine Adun, mai shekaru 40, Oyegoke Olushola (masu tsiro).Mai shekara 42, da kuma Charity Goodluck 29.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Bello Kontongs ya ce wadanda ake zargin sun kware wajen hako kawarwaki cikin kabari a makabarta da kuma yankan sassan jikin Hawa domin kasuwanci.
Ya ce Josephine Adun ita ce shugabar gungun masu aikata laifuka na musamman, yayin da Oyegoke Olushola shi ne ‘dan gandun daji.
Ya kara da cewa Charity Goodluck da ke zaune a titin Forestry na garin Ologbo, ta sayi kokon kan dan adam a hannun miyagun mutanen a kan kudi Naira 40,000.
Kazalika Kakakin rundunar Yan sandan jihar ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kamma gudanar da bincike.
A wani labarin Kuma na daban.
EFCC ta kama mutum 36 da Ake zargin masu damfara ta yanar Gizo ne a Enugu
A jiya Laraba Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC, tace ta kama mutane 36 bisa zargin su da aikata zamba da wasu laifuffuka a yanar gizo a jihar Enugu.
Shugaban sashen kafafen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan Inda yace Jami’yan hukumar shiyar Enugu ne suka kame waɗanda ake zargin.
Hukumar yaki da masu yima tattalin arziki kasa zagon kasa ta bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar haka Chukwuma Destiny, Emenalom Precise, Nwaeze Obinna, Ogbonna Monday, Raymond Chigozie, Mmadu Bright, Chigozie Sixtus, Ike Joachim da Uchechukwu, Ifeanyi Uzor, sai kuma Iwuanyanwu Divine, Nwoke Udojah, Patrick Micheal, Chukwu Hillary, Charles Nneji, Nwachukwu Chibueze, Obinna Ajem, Egwu Williams da kuma Samuel Michael da dai sauran su.
Sanarwa ta kara da cewa an kama wadanda ake zargin ne a Owerri babban birnin jihar Imo bayan samun wasu kwararan bayanai sirri da suka dangantasu da su da wasu Ayyukan damfara a yanar gizo.
Kayyakin da dai aka kwato daga hannun wadan dake zargin sun hada da: wayoyin hannun da dama , Na urorin Kwamfuta , da fasfon din ƙasa da ƙasa.
Sauran sune Mota kirar kirar Marsandi Benze GLK mai lambar rigista KTU 729 HD, da wata mota kirar Toyota Kamri kirar 720 HL.
Kazalika Kakakin Hukumata na EFFC Wilson Uwujaren ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu da zarar an kammala gudanar da binciken.