Wata kotun majistare da ke Kaduna, a ranar Alhamis, ta yanke wa wani mutum mai shekaru 35, Mai suna Waziri Gambo, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin yin sojin gona da wani ma’aikacin kotu.
Gambo, wanda ke zaune a garin Kawo a jihar Kaduna, ya amsa laifin hada baki da aikata wasu laifuka, kuma ya roki a yi masa sassauci.
Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Emmanuel ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar Naira 20,000.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Insfecta Chidi Leo ya shaidawa kotun cewa Wanda ake tuhuma, ya bayyana kansa a matsayin magatakardar kotun, wanda daga bisani aka san karya ne.
Leo ya lura cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 57 da 261 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna.
A wani labari Kuma na daban.
Mataimaki Ga Shugaba Buhari Ya Tabbatar Da Jonathan A Matsayin Mamba Na APC
Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmaad ya tabbatar da sauya shekar Goodluck Jonathan zuwa jam’iyyar APC.
Bashir ya tabbatar da hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani ga masu shakkar hasashen da ya yi a baya na cewa tsohon shugaban kasar zai sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce: “Lokacin da na bayar da labarin shigowar tsohon shugaban kasa Jonathan jam’iyyarmu, magoya bayansa da ba su sani ba sun zage ni cewa hakan ba zai taba faruwa ba ko da a mafarki.
“Ya kamata su sani cewa mun san wani abu da ba su sani ba kuma ba duk abin da aka shirya da aiwatar da shi a shafukan sada zumunta ba.”
Idan dai za a iya tunawa, Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito an ce wata kungiyar arewa ce ta siya wa tsohon shugaban kasa Jonathan fom din tsayawa takara miliyan 100 na jam’iyya mai mulki a ranar Litinin.
Duk da cewa Jonathan ya musanta sanin sayen fom din, a yammacin jiya ne tsohon shugaban kasar ya kai wa shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu ziyara a gidansa da ke Abuja.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar ya je gidan Adamu ne domin neman tabbacin jam’iyyar APC kafin ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki.
Wasu majiyoyi da aka tattauna dasu sun shaidawa Jaridar Daily Post cewa duk da cewa Shugaban jam’iyyar APC na maraba da tsohon shugaban kasar zuwa jam’iyya mai mulki, kwata-kwata babu tabbacin za a iya ba shi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.