Bayan shafe kimanin wata biyu ana gudanar da shari’ar nan ta mutumin da ya kashe wata Matar aure da yarta Yar kimanin shekaru hudu da hai huwa a shiyyar Labana dake Birnin Kebbi na Jihar Kebbi.
Babbar kotun Shari’a ta jiha ta yankewa matshin hukunci kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da akaita laifuka biyu.
Da yake zartas da hukuncin mai shari’a Suleman Muhammad Ambursa ya karanto wa mutumin laifuka biyu da aka same shi da su, wato laifin kisan matar da yarta, kana ya bayyana cewa bisa tanadi doka an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Da yake jawabi ga manema labarai mijin matar da aka kashe Akilu Yusuf ya bayyana jin dadinsa akan hukuncin.
Ya kuma godema Allah subhanahu wata’ala akan nasarar da suka samu a kotu.
Inda yayi kira ga gwamnan jiha da ta taimaka wurin ganin an zartar da hukuncin da aka yanke wa wanda aka kama da laifin.
A zantawar sa da manema labarai lauyan wanda aka yankewa hukunci, Barista Salisu Muhammad Alhasan ya ce, kotu ta yi aikin da ya rataya a wuyanta, kasenwar wanda ake zargin ya aikata laifukan kuma ya amsa laifin.
Sai dai kuma duk da ya bayyana cewa suna da hurumin dau kaka kara, kan hukuncin, Amma lauyan yace ba zai yi magana akan yiyuwar dau kaka karar ba a halin yanzu.
Idan dai ba a manta ba a ranar laraba 20 ga watan Afrilu wannan shekarar ce, Jami’an Rundunar Yan sanda jihar Kebbi suka baje Kolin wani matashi mai suna Idris Sulaiman da ya amsa cewa, shi ne ya shiga har Cikin Gida ya kashe Wata Matar aure da yarta Yar kimanin shekaru hudu da hai huwa, a shiyyar Labana dake Birnin Kebbi na jihar.
Lamarin da ya janyo maganganu da dama a ciki da wajen jihar nan.
.