Wata gobara da ta barke a babbar gadar nan ta Otedola Bridge dake birnin Ikkon Jihar Legas inda ala tilas ta sanya cunkuso a babbar hanyar nan ta Legas zuwa Ibada dda ma saura sassan birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa arangama da aka samu tsakanin wasu tankokin dakon mai biyu da tirela da kuma wasu kananan motoci biyu ne ta haddasa gobarar.
to sai dai ba tare da wata-wata ba ne hukumomin bada agaji kamar na Hukumar Kashe Gobara da kuma Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas LASTMA da dai sauran su sun yi kukan kura wajen ganin an shawo kan matsalar.
Hukumar LASTMA ta wallafa a shafin ta na Tuwita cewa cunkuson ya tilasta maida hanyar nan ta Motorway &-up izuwa Alapere.