Ministan Matasa da bunkasa harkokin wasanni ta kasa Mista Sunday Dare ya kalubalanci tawagar kwallon Kafa ta Super Eagles da kada ta yi sako-sako da tawagar Suirrels ta kasar Jamhuriyar Benin a karawar su ta sharar fagen shiga gasar Kofin Nahiyar Afirka.
Cikin wata sanarwa daga ofishinyada labaran Ministan ta ce dukkan yan Najeriya sun zaku suga cewa tawagar Super Eagles din ta yi nasara kan Squirrels din.
Sanarwa ta ce “Dukkan yan Najeirya suna bayan ku a wannan kafzawa da tawagar Squirrels ta sharar fagen shiga cin Kofin Nahiyar Afirka. Wannan wasa yana da matukar muhimmanci don ku yi duk mai yiwuwa don samun nasara.”
Bugu da kari “Kun fara wannan fafatawa cikin aminci, to ya kamata ku dore da hakan don samun kan ku cikin wannana gasa ta cin Kfoin Nahiyar Afirka”
“Babu wata karawa dake zuwa cikin sauki, babu batun karamar kasa. don haka ba raina abokan karawa saboda kwallo ba tabbasa.
Daga bisani ya ja hankalin yan Super Eagles din da su jajirce wajen ci gaba da kare martabar tawagar kamar yadda aka san ta a baya.