An tura sabon kwamishinan ‘yan sanda (CP), Maiyaki Muhammed-Baba, zuwa jihar Nasarawa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Nansel Rahman, ya fitar, ya ce sabon Kwamiahinan ya karbi ragamar rugudanar ne daga hannun Mista Adesina Soyemi wanda a kwanan nan aka kara masa mukamin mataimakin sufeto Janar (AIG) na ‘yan sanda.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Karyata Rahoton Sauya Shekar Mambobinta 1, 500 A Jigawa
Sanarwar ta kara da cewa sabon CP wanda ya fito daga Bida ta jihar Neja ya shiga aikin rundunar ne a ranar 3 ga Maris, 1990.
Don haka rundunar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su ba shi goyon baya da hadin kai domin samun nasarar aikinsa a jihar.
A WANI LABARIN KUMA: An Kama Wasu Yan Najeriya Da Laifin Safarar Muggan Gwayoyi A Afrika Ta Kudu
An kama wasu ‘yan Najeriya 5 da laifin safarar kwayoyi a birnin Pretoria na kasar Afrika ta Kudu.
Jami’an Yan sandan yankin Tshwane dake yaki da muggan kwayoyi ne TMPD suka kama wadan ake zargin a ranar Talata a Garsfontein