Gwamnatin jihar Ondo a ranar Laraba ta amince da bukatar samar da dokar da za ta samar da rundunar Amotekun a jihar.
Jihar ta Ondo ta amince da shirin da zai samar da hukumar tsaro ta jihar Ondo da kuma rundunar Amotekun zuwa doka.
Donald Ojogo, Kwamishinan yada labaran da wayar da kan al’umma na jihar shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce za a mika zuwa majalisar jihar dokar domin tabbatar da shi da sanya masa hannu inda daga bisani a maishe shi doka.
Ya yi bayanin cewa bayanan dake cikin dokar, Kwamishinan shari’a na jihar shi ne ya gabatar da su inda kuma suka samu sahhalewar membobin zartarwar na jihar.