Gwamna Nyesom Wike ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da yin katsalandan a zaben gwamna na 2019 a jihar Ribas. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Gwamna Wike ya yi wannan ikirarin ne a ranar Larabar da ta gabata yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan cikin gida a garin Igwuruta da ke karamar hukumar Ikwerre ta jihar.
Ya ce shugaban kasa ta bangaren tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi amfani da jami’an tsaro wajen yunkurin murde zaben gwamna.
Gwamnan ya ce al’ummar jihar sun yi watsi da matakin da hukumomin tsaro suka dauka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban Tarayyar Soviet Dake Kalubalantar Putin Kan Mamaye Ukraine Ya Rasu
Ya ce “Na ji shugaban kasa na ya jawabj a jiya cewa ba zai tsoma baki ba (a zaben 2023). Ya shaida wa gwamnonin ba zai tsoma baki ba.
“A daya (2019) kun tsoma baki tare da turo mutane su zo su a jihar Ribas.
“Na gode shugaban kasa da cewa ba za ku tsoma baki ko tsoratar da kowa ba. Ma’ana babu wata hanya ga jam’iyyar ku da zata yi nasara.
“Tabbas ya tsoma baki a karon karshe ta hanyar amfani da sojoji ta bangaren tsohon ministan sufuri amma jama’a suka tashi suka ce a’a hakan ba zai faru ba.
“Na gode wa shugaban kasa da ya ke son barin ganin an gudanar da zaben gaskiya da adalci”.
A WANI LABARIN KUMA: Kano: Duk Wata Ana Kwashe Tifar Shara 1,500 Don Gujewa Matsalolin Muhalli – Getso
Kwamishinan muhalli na jihar Kano, Kabiru Ibrahim Getso, ya ce dumamar yanayi da gini kan mugudanan ruwa ne yake haddasa ambaliyar ruwa a jihar dama duniya baki daya.
Dr Getso ya bayyana haka ne yayin ziyarar da yakai majalisar dokokin Kano don tattauna abubuwan da suka shafi muhalli a jihar.