- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana ra’ayinsa game da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar
- El-Rufai ya ce al’ummar Jamhuriyar Nijar ɗaya ne da waɗanda ke zaune a Arewacin Najeriya
- Tsohon gwamnan ya bukaci ECOWAS da ta “juya haka don gujewa yaƙin basasa tsakanin ‘yan’uwa”.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Talata, 22 ga watan Agusta, ya gargaɗi kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS) kan yin yaƙi da Jamhuriyar Nijar da ta yi juyin mulki.
El-Rufai ya lura cewa “Jamhuriyar Nijar ɗaya ce da waɗanda ke zaune a Arewacin Najeriya”.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa ECOWAS ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ya kamata “a guji wannan yakin basasa tsakanin ‘yan’uwa”.
El-Rufai na hannun damar shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS a halin yanzu. Ya rubuta:
“Yayin da ECOWAS ke buga ganguna na yaƙi, na tuna da 1970s rock classic by Dire Straits – ‘Brothers in Arms’, domin yaki a yankin mu yaki ne tsakanin ‘yan’uwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Shettima Ya Shilla Kasar Waje Domin Wakiltar Tinubu a Wani Muhimmin Taro
“Hakika al’ummar Jamhuriyar Nijar daya ne da wadanda ke zaune a Arewacin Najeriya. Don haka mu karkata a baya don guje wa wannan yaƙin basasa tsakanin ’yan’uwa.”
Ba Za Mu Ƙyale Shanu A Cikin Abuja Ba: Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike
A wani labarin kuma: Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabon ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwo a fili a cikin Abuja, inda ya ce ba za a iya jurewa irin wannan.
A cikin wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa, Wike ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tuntuɓi makiyaya, yana mai cewa, “Ba za mu bar shanu a cikin Abuja ba”.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, jim kaɗan bayan rantsar da shi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
Jaridar Vanguard ta kuma ƙara da cewa, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce makiyaya za su iya kiwon shanu a wajen birnin amma kuma ba za a bari su ci ciyawar da ake amfani da ita wajen ƙawata birnin ba