Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya shawarci Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da ya mayar da hankali kan aikinsa na mulkin jihar ta Arewa maso Yamma.
Matawalle ya ba da wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ya na mai da martani ne kan wasu zarge-zargen da Dauda ya yi game da zamansa a matsayin gwamnan jihar.
Zargin ya shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma, basussuka masu yawa da kuma rashin biyan jarabawa da kudin makaranta na dalibai na gida da waje da dai sauransu.
Karanta nanGobara Ta Lakume Kayan Miliyoyin Kudade A Maiduguri
Ina ganin mutumin bai shirya yin mulki ba a kullum sai ya canja zarge-zarge a maimakon shi ya tattara hankalinsa ya kuma tabbatar da cewa ya samar da dimokuradiyya ga al’ummar Zamfara.
Yakan yi fada ne kawai,gwamnoni nawa ne suka mulki jihar hudu ko biyar daga cikin mu,tsawon shekarun da suka gabata babu wanda ya waiwaya baya ya yi kokarin lalatar da magabata, amma wannan maimakon ya mayar da hankali kan lamarin tsaro sai ya rika wasa da zargi.
Lokacin da aka yi garkuwa da daliban Jami’ar Gusau, Shugaban kasa ya umurci dukkan mu da jami’an tsaro da mu je wurin mu jajantawa al’ummar jihar da kuma iyaye.
Ba ya cikin jihar ya tafi yawo muka kira shi, bai amsa ba,sai da muka bi hanyoyi kafin mu samu lambar wayarsa muka kira shi.
Ya roki Ministan cewa ba ya nan, amma da zarar ya zo, zai fada mana. Wannan tawaga ce da shugaban kasa ya ba da umarnin zuwa jihar har yau, babu wani labari daga gwamnan.
Shawarata a gare shi ita ce, ya tuna cewa an zabe shi ne domin tunkarar al’amuran jiharsa. A matsayina na magabacin Dauda, a koyaushe ina yi masa addu’ar samun nasara, ya tabbatar da cewa batun rashin tsaro, ta’addanci da ‘yan fashi sun zama tarihi a jihar.
Saboda ko mene ne, jihata ce, iyalina da kowa da kowa yana wurin, ciki har da dangina don haka, a kullum ina addu’a a kullum don Allah ya kare mu daga irin wannan yanayi.
Allah ya sani na yi iya ƙoƙarina kuma zan yi duk iyakar kokarina ga Nijeriya, muna aiki tuƙuru don ganin cewa duk wasu laifuka sun tafi,na ga ya kamata ya zauna ya yi nazari mai zurfi, kuma zai san cewa mutanen da suke yi masa nasihar kuskure makiyansa ne.
Ministan ya ce ba zai sake mayar da martani ga gwamnan ba kamar yadda kungiyar dattawan Arewa da ‘yan sanda suka ba shi shawarar kada ya yi.
A wani labarin kumaGwamna Hope Uzodimma Na Jam’iyar APC Ya Lashe Zaben Jahar Imo
Bari ya ci gaba da fadin duk abin da yake so na fadi nawa muna da abubuwa da yawa da za mu faɗa game da shi waɗanda ba zan faɗa ba saboda dattawan mu sun yi magana a kai. Ina girmama su kuma zan tabbatar da cewa na mutunta abin da suka shawarce ni in yi.
Zan mayar da hankali wajen tabbatar da cewa mutanen Arewa maso Yamma sun kubuta daga wadannan miyagu. Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na shugabannin yankin.
Ya kara da cewa (NAN) ya kamata mu hada kai mu yaki wadannan miyagu tare maimakon fada da junanmu inji Matawalle.