Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya ce har sai an gyara tsarin zaben kasar nan domin hana sayen kuri’u,amma idan ba a dauki wani mataki ba Nijeriya zabe a Nijeriya zai zama kamar cin Kasuwa.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Lahadi yayin da yake mayar da martani kan rahotannin sayen kuri’u da suka kawo cikas a zaben gwamnoni da aka gudanar ranar Asabar a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa.
Karanta nanGwamnatin Jahar Osun Ta Karyata Batun Karin Albashin 25,000 Ga Ma’aikata
Jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan siyasa a ranar Asabar bayan da aka kama su da makudan kudade, ana zarginsu da sayen kuri’u.
A cewar Shehu Sani, idan kasar ta ci gaba da tafiyar da tsarin dimokuradiyya da ke karfafa sayen kuri’u, masu kudi ne kawai za su ci gaba da mulki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa,matukar za mu gudanar da tsarin dimokuradiyya wanda zai karfafa tare da amincewa da yin amfani da kudi wajen siyan kuri’un wakilan jam’iyya da kuma sayen kuri’un al’umma.
To zabe a Nijeriya zai kasance ne kawai ga mutanen da za su iya zuba kudadensu su sayi kuri’u ba tare da wata matsala ba.
A wani labarin kumaKa Ji Da Aikin Dake Gabanka,Ka Bar Bata Mani Suna-Matawalle Ga Dauda Lawal
Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya shawarci Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da ya mayar da hankali kan aikinsa na mulkin jihar Arewa maso Yamma.
Matawalle ya ba da wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ya na mai da martani ne kan wasu zarge-zargen da Dauda ya yi game da zamansa a matsayin gwamnan jihar.
Zargin da ake zargin ya shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma, basussuka masu yawa da kuma rashin biyan jarabawa da kudin makaranta na dalibai a gida da waje da dai sauransu.