Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ce bai kamata yan Najeriya su bari shugaban kasa ko gwamnonin jahohi su rika tsorata su ba.
Sanusi, wanda shi ne Shugaban darikar Tijjaniyya, ya ce ’yan Najeriya ba wawaye bane don haka suka zabi yin watsi da siyasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, tsohon gwamnan babban bankin kasar ya ce yan Najeriya ba za su samu kasar da za su kira tasu ba idan har suka kasa fita daga kangin shugabannin siyasa.
A cewar Sanusi wani ba zai iya tsoratar da mu ba saboda kai shugaban kasa ne ko kuma kai gwamna ne kuma ba za mu iya gaya maka cewa ka yi kuskure ba.
KARANTA NANRashin Tantance El Rufai A Matsayin Minista Babbar Asara Ce Ga Arewa-Lukman
Mun zabi sassa daban-daban. Da na shiga siyasa, a kalla idan aka ba wa mutanen da ke da damar zama shugaban kasa a Najeriya, zan iya zama shugaban kasa ko kuma na zama gwamna.
Kawai don na zaɓi inki shiga siyasa ba yana nufin ni ba ɗan adam bane. Wannan shi ne abin da ya kamata mu koya a matsayinmu na ’yan Najeriya. Muna shan wahala da yawa, kuma duk muna jin tsoro a wuraren jin daɗinmu.
A lokacin da waɗannan mutanen za su gama da mu, yaranmu ba za su sami inda za su kira wata ƙasa ba.hanya daya tilo da za mu kwato al’ummarmu, mu baiwa ‘ya’yanmu makomar da ta kamace su, idan ba ku cikin siyasa, to ku rike wadanda ke cikin siyasa.
Ba yanayi mai dadi ba ne kasancewa a ciki siyasa,amma lokaci yayi da mutane zasu gane yancinsu kuma su mai da hankali wajen kwato abinda yake nasu.
A WANI LABARIN KUMAGwamna Radda Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Alkalan Jahar Katsina
Don haka ya kamata mutane su san halin da suke ciki kuma su hankalta akan abinda ka iya zuwa wanda basu da maganinshi.