- Hukumar NDLEA reshen babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama kimanin kilogiram 3,091.032 na haramtattun kwayoyi da kudinsu ya haura Naira miliyan 56.9
- An kama mutane 343 da ake zargi da shan miyagun kwayoyi a cikin tsawon lokacin da ake bincike
- A cikin haramtattun muggan kwayoyin da ake cafkewa tabar wiwi ita ce aka fi kamawa
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa,reshen babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama kimanin kilogiram 3,091.032 na haramtattun kwayoyi da kudinsu ya haura Naira miliyan 56.9 tsakanin watan Janairu zuwa yau.
Mista Kabir Tsakuwa, Kwamandan babban birnin tarayya Abuja ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Laraba a Abuja.
KARANTA WANNAN: Babu Wata Jami’ar Tarayya da Aka Yarda Ta Karbi Kuɗi – FG
Tsakuwa ya ce haramtattun muggan kwayoyin da aka kama sun hada da wasu da ake zargin tabar wiwi, hodar iblis, Methamphetamine, Heroin, Tramadol, Rohypnol, Diazepam, Ecstasy, da kuma Megadon.
Ya kuma bayyana cewa, an kama mutane 343 da ake zargi da shan miyagun kwayoyi a cikin tsawon lokacin da ake bincike, inda ya ce sun hada da maza 328 da kuma mata 15.
Tsakuwa ya kuma ce, a cikin lokacin da ake wannan nazarin, an gurfanar da masu laifin safarar miyagun kwayoyi 188 a gaban kuliya, yayin da 126 aka yanke musu hukuncin dauri daban-daban.
A cewarsa, daga cikin kilogiram 3,091.032 na haramtattun kwayoyi da aka kama tsakanin watan Janairu zuwa yanzu, tabar wiwi ita ce aka fi kamawa.
Tsakuwa ya ce, “Haramtattun kwayoyin da aka kama sun hada da tabar wiwi kilogiram 3,022.529, hodar iblis kilogiram 0.114 Methamphetamine kilo 1.25, Heroin kilo 0.0021.
“Mun kuma kama wadanda ake zargin Tramadol kilogiram 18.578, Rohypnol kilogiram 1.195, Diazepam kilogiram 4.471, Ecstasy kilo 0.113 da Megadon kilo 0.263.
“Kuɗin waɗannan haramtattun miyagun kwayoyi ya kai kusan Naira Miliyan N56, 903, 600 kawai.”
Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce an yiwa mutane 33 masu fama da matsalar shan miyagun kwayoyi gyara, yayin da 102 masu shan muggan kwayoyi aka yi musu nasiha tare da sakin su a cikin wannan lokaci.
Tsakuwa ya kara da cewa hukumar tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro za su shiga aikin hadin gwiwa a cikin babban birnin tarayya Abuja domin kakkabe rumfuna da wuraren zafi a babban birnin tarayya Abuja.
Wadannan, in ji shi, su ne wuraren da ake zargin shan muggan kwayoyi da aikata laifuka suna da yawa.
NAN
A wani labarin kuma, Tinubu Ya Gaji Mawuyacin Tattalin Arziki daga Tsohon Shugaba Buhari – Oshiomole
Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, a ranar Litinin, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya gaji mummunan yanayin tattalin arziki daga gwamnatin da ta shude ne.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin hukunce-hukuncen da gwamnatin shugaba Tinubu ta dauka su ne matakin farko na sake fasalin tattalin arziki.