Kungiyar Cislac da ke yakar cin hanci da rashawa a Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin yaki da cin hancin kan su dinga mayar da kadarorin da suka kwato daga kasashen ketare ga asalin jihohin aka sace musu kudin.
Shugaban kungiyar Comrade Auwal Musa Rafsanjani ne ya bayyana hakan yayin wani taro da suka gudanar a kasar Kenya, wanda yayi duba kan irin kadarorin da kasashen musamman a Afrika ke kwatowa daga sassan duniya.
KARANTA ANAN: Yawancin hanyoyin Najeriya sun Lalace – FERMA
Ya bayar da misali da jihar Delta wadda a kawanakin baya gwamnatin tarayya ta kwato daga kasar waje, amma maimakon a mayarwa da jihar sai gwamnatin tarayya ta rike a matsayin tata, wanda hakan ya sa CISLAC ke cewa babu adalci a hakan.
Daga nan sai kungiyar ta bukaci kasashen Afrika kan samar da wani tsari kan irin kadarorin da suke kwatowa, bayan barayin jihar sun sace tare da ficewa waje da su.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da majalisar kasa kan yin abinda ya kamata wajen tabbatar da cewa jihohi na samu duk dukiyar su da wasu bata garin kan mallake ba bisa ka’isa ba, domin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma samar da Karin ayyukan more rayuwa ga jihar.
A wani labarin kuma: Ku Jefar da Sunayen Alkalan da kuka gani an naɗa don Jagorantar Ƙararrakin Zaɓen 2023 — Kotu
Hukumomin shelkwatar kotun daukaka kara da ke Abuja sun fayyace cewa har yanzu ba su fitar da sunayen alkalan da za su kula da kararrakin da ka iya tasowa wajen gudanar da zabukan 2023 a kasar nan ba.
Hukumomin a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja sun shawarci jama’a da su yi watsi da duk wani jerin sunayen da ake zargin ana yadawa a shafukan sada zumunta a matsayin sahihan jerin alkalai.
Comments 1