Kaduna: Hakanan Jirgin Saman NAF yaƙi Ƙaddamar da hari ga Ƴan Ta’adda lokacin suke kashe mutane — Shehu Sani
Tsohon Ɗan Majalisar Dattijai Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani ya bada jawabi kan harin da ƴan ta’adda a kudancin Kaduna.
Ƴqn ta’adda dai sun kai hari a yankin a ranar Laraba tare da kasje mutane sama da 30.
A Wani rahoto yace a wannan lokacin ƴan Ta’addan sun zone da Jirgi mai saukar angulu, inda suka gudanar da harin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu: Buhari zai miƙa Mulki ga wanda yafi dace wa ya Gaje shi — Inji Uzodimma
Amma Gwamnatin Jahar Kaduna a ranar Alhamis ta ƙaryata rahoton kai harin ƴan Ta’addan da jirgi, amma ta tabbatar da mutuwar mutane 32 a harin, daya wakana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jahar.
Tace Jirgin da aka gani na Rundunar Sojin Sama ne, wanda yazo domin faɗa da ƴan bindigar.
Sama da ƴan bindiga 159 suka yiwa ƙauyen ƙawanya akan Babura, tare da ƙona gidaje da dama, a yayinda suka ƙaddamar da harin ga talakawa.
Shehu Sani wanda ya tabbatar da kisan yace Jirgin Sojin Saman bai kai wani hari akan ƴan ta’addan ba.
“Na kira Shugaban Matasa na Kajuru ya tabbatar mani da kisan mutane 32 a Kaduna.
“Jirgin mai yiwuwa bana ƴan Ta’adda bane, amma hakanan yaƙi kai hari ga ƴan Ta’addan a lokacin da suke kisan da ƙone gidajen mutane,” Inji shi
Comments 1