Kaduna: Matan Ƴan Sanda sun gudanar da Azumi, addu’o’i kan hare-haren Ƴan Bindiga
Kungiyar Matan Jami’an Ƴan Sanda (POWA) reshen Jihar Kaduna, ta yaba da Addu’o’i kan hare-haren ‘yan bindiga a Kaduna da kewaye.
Matar Babban Sufeto-Janar na Ƴan Sandan Najeriya, Hajiya Hajara Alkali Baba Usman, a kwanakin baya ta umarci ‘yan kungiyar ta POWA da su gudanar da azumi da addu’o’i na kwanaki biyu domin neman taimakon Allah kan hare-haren ƴan bindiga a fadin kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Tikitin Peter Obi/Baba-Ahmed Yafi kowane nagarta – Gamayyar Ƙungiyoyi
Bayan haka, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce matan jami’an sun gudanar da azumi da addu’o’i a kan ci gaba da kai hare-hare da miyagu ke yi kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, mazajensu.
Ya ce an fara zaman addu’ar ne domin babu wani zabi da ya wuce a yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya kama wadanda suka yi kisan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Addinin wanda shugabar kungiyar POWA ta jiha kuma uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Alhaja Salimat Tinuke Ayoku ta jagoranta, ta dukufa wajen samar da zaman lafiya a Najeriya, saboda kalubalen tsaro da aka fuskanta a baya-bayan nan.
A yayin zaman addu’ar, sun yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalolin tsaro da ke addabar jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya