Shugaban jamhuriyyar Nijer, Mahamadou issoufou ya jinjinawa jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) dake garin Maradi a kasar, inda ya ce kafa jami’ar a kasar ya bunkasa bangaren zamantakewa da kuma tattalin arzikin kasar, sannan har wala yau jami’ar ta kawo ci gaba ta fuskoki daban-daban a kasar.
Shugaba Issoufou ya bayyana hakan ne a lokacin da wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da tawagarsa suka kai wa shugaban ziyara a fadar gwamnati dake birnin Niamey a ranar Asabar.
Shugaban har wala yau ya ce kafa jami’ar a garin Maradi ya bunkasa ci gaban ilimi tare da habaka tattalin arzikin jihar da ma kasar baki daya.
A na shi jawabin, shugaban MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana jindadinsa bisa goyon bayan da jami’ar take samu daga gwamnatin Jamhuriyyar Nijer. Inda ya jaddada bukatar jami’ar na ci gaba da bada gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma’aikatanta, dalibai da ma makwabtan jami’ar.