Kakakin Majalissar da aka tsige ya Garzaya zuwa kotu
Kakakin Majalissa Oluomo wanda aka tsige a Ogun ya garzaya kotu.
Tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun Olakunle Oluomo ya ce ya shigar da kara a gaban Babbar Kotun Jihar yana kalubalantar tsige shi da aka yi.
Olakunle ya magantu ne akan shigewar bayan da wata gidan Jarida ta bayar da rahoton rashin mayar da martani da kuma ƙin yin tsokaci kwanaki uku da tsige shi ba zato ba tsammani a matsayin Shugaban Majalisar.
Shugaban Majalisar wanda aka tsige a ranar Talata bisa wasu laifuka da suka shafi girman kai da ƙyaliya da dai sauransu ya dage cewa tsige shi bai bi ka’ida ba, dalilin da ya sa ya garzaya kotu kenan.
KARANTA NAN:Ba zan taɓa bari a bada belin masu garkuwa da mutane a Abuja – Wike
‘Yan Majalisar 18 daga cikin su 26 ne suka tsige Oluomo wanda Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin almundahanar kudi har Naira biliyan 25.
Da yake mayar da martani kan zargin da ake masa Oluomo ya ce ya kai abokan aikinsa gaban kotu yana mai jaddada cewa tsige shi da aka yi ba bisa ka’ida ba ne.
Sai dai ya ce bai samu goyon bayan takwarorinsa ba tun bayan dawowarsa a matsayin Kakakin Majalisar a karo na biyu.
Don bayanin ku na shigar da ƙara a babbar kotun Jihar Ogun inda nake neman kotu ta tabbatar da ko za a iya tsige kakakin Majalisa ta hanyar zamba ko juyin mulki irin haka, sai kuma kotun ta ce su je su ƙara haɗa bayanan hujjoji wanda ya dace su dawo a ranar 7 ga watan Fabrairu don kare karar mu.
Ni mai imani ne da abinda doka da oda ta tsara, shiyasa na garzaya kotu ban damu da adadin mutanen da suka sanya hannu domin bin ka’ida ba sun ba ni sanarwa ranar Laraba kuma har zuwa gobe (Asabar) zan amsa amma Na amsa yau.
Don haka ina neman zaman lafiya, shi ya sa na garzaya kotu domin a tantance ko suna da ikon tsige ni kamar yadda suka yi.
A wani labarin kuma:Ƴan sanda sun ki karɓar cin hancin N1m da wani mai garkuwa da Mutane ya basu
‘Yan sanda sun ki karɓar cin hancin N1m da wani mai garkuwa da Mutane ya ba…….