Kashe-kashe a Plateau: Gwamna Mutfwang ya sassauta dokar hana fita a Mangu
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a karamar hukumar Mangu da ke jihar bayan hare-haren baya-bayan nan.
Mista Gyang Bere, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Jos.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnan Kwara Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Kasafin Kudin 2024
A cewar sanarwar, a yanzu za a sanya dokar ta-baci tsakanin karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma a kowace rana, har sai an samu labari.
Gwamnan ya kara da cewa, an yi bitar ne saboda ingantuwar yanayin tsaro da aka samu a yankin, inda ya ce an yi ta tattaunawa da shugabannin addini da na al’umma kan matsalar tsaro a yankin.
“Bayan an samu ci gaba a harkar tsaro da kuma tuntubar kwamitin tsaro na Jiha, an sassauta dokar hana fita.
“Don haka ina kira ga mazauna garin Mangu da su kiyaye dokar hana fita kuma su guji daukar doka a hannunsu.
Mutfwang ya ce “Muna karfafa jami’an tsaro da su aiwatar da dokar ta-bacin don gujewa tabarbarewar doka da oda.”
Gwamnan wanda ya godewa mazauna yankin bisa hadin kan da suka ba su ya zuwa yanzu, ya bukace su da su bada hadin kai da goyon bayan jami’an tsaro a yunkurinsu na ganin an samu zaman lafiya a Filato.
A wani labarin kuma:Gwamnan Kwara Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Kasafin Kudin 2024
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin ba zai taɓa bari a ba da beli masu garkuwa da mutane ba.
Wike ya ce zai tabbatar da cewa an hukunta masu garkuwa da mutane kamar yadda doka ta tanada.