Hukumar Ƴan Sandan farin kaya, ta gargaɗi ƴan siyasa a kan furta kalaman tinziri da za su iya haifar da tashin hankali a cikin al’umma.
Kakakin Hukumar ta SSS, Peter Afinanya ne ya yi gargaɗin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Kashe Mutum guda tare da Garkuwa da 10 a Kaduna
Ya ce gargaɗin ya zo ne sakamakon kalamai marasa dacewa da Shugaban jam’iyar adawa ta PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu ya yi a kan jami’an tsaro, har da hukumar SSS ɗin.
Afunanya ya ce shugaban jam’iyyar, a wani taro kwanan nan a Owerri ranar 23 ga watan Fabrairu, an rawaito ya na cewa PDP ba za ta yi amfani da jami’an SSS domin ta riƙa cin mutuncin al’umma ba idan ta kafa gwamnati a 2023.
Ya ce duk da cewa Hukumar SSS ba ta shiga harkokin siyasa, amma dai abinda Ayu ya faɗa ba daidai ba ne kuma bai dace ba.
A cewar sa, a matsayin Ayu, wanda ya yi Shugaban Majalisar Dattijai, ya kuma yi minista ba sau ɗaya ba sau biyu ba, ya kamata a ce ya san cewa Hukumar ba ta cin zarafin al’umma tunda ta re ya yi aiki da su.
Kakakin ya ƙara da cewa Hukumar na iya bakin ƙoƙarinta ta nisanta kanta wajen tsoma baki a harkokin siyasa, inda ya ce SSS ba ta kyale duk wani jami’in ta da ya karya dokokinta da dokokin ƙasa.