Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Litinin ya mika ta’aziyya ga masarautar Kazaure da ke jihar Jigawa bisa rasuwar Alhaji Ilyasu Adamu, Tafidan Kazaure.
Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Garba Shehu ya fitar, ya bi sahun masarautar da iyalan Adamu wajen addu’ar Allah ya jikan shugaban al’umma da ya rasu Wanda kuma shine Tsohon mataimakin darakta mai kula da harkokin jin dadin jama’a a ma’aikatar lafiya da ci gaban jama’a ta Jigawa.
‘’Ayyukan jin kai da Marigayi Tafidan Kazaure ya yi sun sa jama’a su kaunace shi, kuma mutanen da suka yi mu’amala da shi kai tsaye za su yi kewar sa a Jihar Jigawa da sauran su.
“Allah ya ba shi Jannatul Firdaus,” in ji shugaban kasa Muhammadu Buhari.