Wata kungiya mai suna Citizens Action for Change wanda aka fi sani da CAC a takaice ta jinjinawa rundunar ‘yan sanda bisa matakin da suka dauka na kame duk wani jagororin ‘yan shi’a da mabiyansu a sassan Nijeriya.
Sufeton Janar na ‘yan Sanda, Mohammed Adamu ya bai wa dukkanin jami’an tsaron ‘yan sanda da su tabbata sun kama jagororin ‘yan shi’a da kuma rusa musu muhallansu. Wannan umurnin Sufeton Janar na ‘yan Sandan ya ba da shi ne a ranar 30 ga watan Agustan 2019, inda ya ce jami’ansu ba za su bari ‘yan shi’ar su karya dokar kotu ba.
Shugaban kungiyar ta CAC, Ayokunle Bakare, a wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, ya ce; akwai bukatar gwamnati ta fadada wannan matakin na ta zuwa ga masu fafutikar ganin sun kafa kasar Biyafara wanda aka fi sani da IPOB. Ayokunle Bakare, ya ce; akwai bukatar jagororin ‘yan shi’a su mika kan su domin a yanke musu hukunci daidai da laifin da ake zarginsu.