Kamfanin Ɗangote ya musanta Sauke Farashin Siminti
Kamfanin Dangote ya musanta ikirarin rage farashin Siminti zuwa Naira 2,700 kan kowane buhu mai nauyin kilo 50 maimakon tsohon farashin na baya Naira 5,500.
Mai magana da yawun rukunin Kamfanin Ɗangote Anthony Chiejine ne ya bayyana hakan ga DAILY POST a Safiyar Ranar Litinin.
Chiejine ya bayyana ikirarin a matsayin labarin ƙanzon kurege.
Labari ne na karya,” in ji shi a cikin wani martani mai zafi da ya mayar, kamar yadda Dimokuraɗiyya ta gano.
Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Kamfanin Ɗangote zai zaftare farashin Siminti da kashi 50 cikin 100 daga ranar 1 ga Oktoban shekarar 2023.
Tun da farko Bahir Ahmad mai taimaka wa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai ya yi tsokaci cewa rahoton karya ne.
KARANTA WANNAN LABARIN:NLC ta fara fuskantar turjiya daga wasu ƙungiyoyi kan tsunduma yajin aiki
Ahmad ya bayyana hakan ne a dandalinsa na Sadarwar zamani X wato Twitter da aka fi sani a ranar Lahadi.
Kamfanin Ɗangote ya musanta rahotannin da ake yaɗawa na cewa ta rage farashin siminti daga N5,500 zuwa N2,700 daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Ana sayar da buhun Siminti mai nauyin kilogiram 50 tsakanin N4 600 zuwa N6,000 a Jihohin Legas da Ogun da Ondo da kuma Abuja.
Sai dai kuma makonni biyu da suka gabata, kamfanin Simintin BUA ya bayyana shirin rage farashin buhun Siminti mai nauyin kilogiram 50 zuwa tsakanin N3,000 zuwa N3,500.
Shugaban BUA Abdul Samad Rabiu ne ya bayyana hakan bayan ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A wani labarin kuma:Yadda Ƴan Sanda Suka Yi Awon Gaba Da Ƴan Fashin Jigawa 7 A Jigawa
Yadda Ƴan Sanda Suka Yi Awon Gaba Da Ƴan Fashin Jigawa 7 A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wasu barayi bakwai da wani mai gadin makaranta bisa laifin satar kadarorin makarantar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce, “A ranar 14/9/2023 da misalin karfe 5, jami’an sa ido na sashen Kiyawa sun kama wani Aminu Abdullahi mai shekaru 30 a kauyen Balagu da ke karamar hukumar Kiyawa da wata saniya da ake zargin an sace ta.