Kamfanin sadarwa na Facebook ya toshe shafin sojojin mulki a Myanmar daga dandalin nasa.
Kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya aminta cewa “haɗarin barin shafukan sojojin a Facebook da Instagram na da girma sosai”.
Sojojin sun yi amfani da Facebook wurin yaɗa farfagandar cewa an yi maguɗi a zaɓen 2020 da aka yi a ƙasar.
Rabin al’ummar Myanmar ne ke amfani da Facebook, inda wasu da dama ke ɗauka a matsayin intanet baki ɗaya.
Tun farko Facebook ya fara rufe babban shafin gwamnatin sojojin saboda karya ƙa’idojin dandalin biyo bayan juyin mulkin.