Daga Sulaiman Musa
Tsohon mambar majalisar wakilai kuma shugaban jami’ar Achievers, Owo a jihar Ondo State, Dr. Bode Ayorinde, ya bukaci kungiyoyin addini da su himmatu wajen gina kamfanonin da za su kasance masana’antu domin samar wa mambobinsu ayyukan yi.
Ayorinde, yana mai bayyana cewar ta hakan za a samu damar fitar da wasu mabiya daga matsatsin tattalin arziki, yana mai cewa idan hakan ta faru kuwa addinin ma zai fi yiyuwa a wajen mabiyan.
Ayoŕinde, wanda ke magana a yayin babban taron jami’ar karo na 10, ya kuma kalubalanci gwamnoni da su ma su dukufa wajen gina kamfanoni domin kara samar da hanyoyin aikin yi ga mabiyansu.
Kan matsalar tsaro kuwa, tsohon dan majalisar ya bayyana cewar abun damuwa ne matsalolin tsaro wanda akwai bukatar daukan matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar.
Ya bayyana cewar muradinsa na ganin an kyautata Nijeriya ne ya sanya yake maida hankali kan jami’ar, yana mai cewa a zangon karatu nag aba jami’ar za ta yi kokarin kara samar da tallafin karatu wa dalibai 500.
Mukaddashin shugaban jami’ar Prof. Samuel Aje, ya bayyana cewar dalibai 225 ne suka samu tallafin karatu a jami’ar cikin shekaru uku.