Daga Sulaiman Musa
Wasu ‘yan bindiga dadi sun yi garkuwa da mutane 35 tare da jikkata wasu a wani sabon harin da suka kai wa kauyukan Chiri, Gini da Fuka da suke kananan hukumomin Shiroro da Munya a jihar Neja.
Wannan harin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da mataimakin gwamnan jihar Ahmed Ketso ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gwada a karamar hukumar Shiroro tare da nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar.
Majiyarmu ta gano cewa ‘yan bindigan sun mamaye kauyukan ne a kan Babura a ranar Asabar inda suka yi ta harbin kan mai-uwa da wabi, yayin da kauyawan aikin kuma suka gudu zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Shugaban kungiyar Niger Concerned Citizens, Alhaji Muhammad Awaisu Wana, shine ya tabbatar da faruwar wannan lamarin a cikin wani shirin gidan rediyo a Minna.
Wana ya ce kauyuka 10 daga cikin 15 da suke karamar hukumar Shiroro yanzu haka suna karkashin ikon ‘yan bindiga, ya kuma ce akwai ‘yan gudun hijira sama da 80,000 a jihar.
Daga bisani ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo wa jihar Neja dauki domin shawo kan wannan matsalar na tsaro da ke kara ta’azzara.
Har-ila-yau, daga daga cikin jagororn kungiyar matasan Shiroro, Sani Abubakar Kokki, ya tabbatar da wannan harin na al’ummomi uku da aka kai.