Kana ajiye Okowa, to kaman ta da Ƙuri’un Inyamurai – Ohaneaze ta gargaɗi Atiku
An Gargaɗi Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar akan wani shiri na ajiye Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar sa.
Akwai raɗe-raɗin dake yawo cewa Atiku na shan maganganu daga Gwamnoni na ya ajiye Okowa, tare da musanya shi da Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya zata ɗauki ƴan Najeriya Miliyan 1 aikin Ƙidayar Al’umma ta 2023 — NPC
Haka zalika, magoya bayan Wike suma suna cigaba da nuna bukatar a sanya Wike indai ana Son zaman lafiya a Jam’iyyar.
Amma a cikin wata sanarwa da Majiyar mu ta samu a ranar Talata daga Ƙungiyar Matasa ta Ohaneaze Ndigbo OYC, sun ce Atiku ya ajiye Okowa akan buƙatar kanshi.
Sanarwar mai ɗauke dasa hannun Shugaban ta Mazi Nnabuike da Sakataren ta Comrade Obinna Achionye sun ce duk wani yunƙuri na canja Okowa zai janyo wasu abubuwa.
Kungiyar Inyamurai tace yankin Kudu maso Gabas bazai taɓa yarda ya faɗi gaba ɗaya, tunda ya rasa haifar da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a PDP ko a APC.
“Babu Buƙatar canja abinda muka yi tunanin PDP da APC zasu kai Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa ga yankin Kudu maso Gabas, amma hakan bai samu ba.
“Duk da wannan an riga an wuce dashi, abinda kaɗai ya rage mana shine zaɓin Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar, ta la’akari da cewa Okowa Inyamuri ne cikakke.