A kokarinta na Yaki Da Mummunar da Ta’adar Nan ta sha da ta’ammali da Miyagun Kwayoyi Gwamnatin Jihar Kano ta Kaddamar Da Jakadun Yaki Da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Mata a yankin karamar hukumar Takai.
Da take Jawabi tun da Farko Shugabar Kwamitin Kuma mai Bawa Gwamna Shawara Akan Harkar Lafiya Dr Fauziyya Buba Idris wadda Sakatariyar Kwamitin ta wakilta Hajia Amina Haruna Shanono ta ce Duk Wanda Yake ta’ammali da Miyagun Kwayoyi to babu Shakka zai Tsinci Kansa cikin mutanen da ba a taba Ganin kimarsu a tsakanin Al-umma.
DUBA WANNAN LABARIN:Dalibai da dama zasu amfana da Horon zama Manoman Zamani – Inji Kashifu Inuwa
Mataimakiyar kwamandan Hisba bangaren Mata malama ummalkhulsum Kasim ta yi Jawabi Mai tsawo game da illolin Shaye Shaye a Mahangar Addinin Musulunci.
Anata bangaren Mataimakiyarta Shugabar Kwamitin Kuma Wakiliyar Me Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Hajiya Yardada Maikano Bichi ta Kira ga Iyaye Mata na yankin da su qara Sanya idanu wajen Tarbiyar Tarbiyar Yaransu.
Jami’in yada labaran Kwamitin Auwalu Musa Yola ya tabbatarwa da jaridar Dimokuradiyya cewa An gudanar da Taron ne a Babban Dakin Taro dake Garin Takai, a inda aka Karkare da bada lambar yabo ga me Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.
Comments 1