Hukumar yaki da aikatawa rashawa da dangoginsu ta ICPC ta fara bincike kan wani korafi da wasu jami’an hukumar KAROTA suka shigar mata bisa zargin shugaban hukumar Baffa Babba Ɗan’agundi da rashawa.
Jami’an hukumar dai sun zargi Baffa da amfani da takardun bogi mallakin kansa wajen karbar tarar da aka ci masu ababan hawa, tare da yin kwana da kudin tarar maimakon turawa gwamnati kai tsaye.
Takardun (Receipts) din suna fara fitowa ne daga shelkwatar hukumar inda daga bisani aka raba su zuwa sauran kotunan tafi da gidan ka da hukumar ta samar a wasu sassa na jihar Kano.
Kazalika cikin korafin nasu sun kuma zargi Ɗan’agundi da dauko wani dan’uwansa mai suna Shehu, wanda kuma ba ma’aikacin gwamnati bane wajen dora shi akan harkar lamarin da suke ganin cewa akwai sake cikin lamarin.
Jaridar Dimokuraɗiyya tayi kokarin samun shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi abun ya ci tura, amma wakilin mu na Kano ya samu ganawa da mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Naisa amma ya bayyana masa cewa bashi da masaniya kan batun amma ya jira shi zuwa ranar Litinin domin ya bincika tare da yi masa karin haske.