Kwamitin da uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta turo domin karbar korafin zaben shugabannin jam’iyya na Kano daya gudana ranar asabar 16 ga watan oktoba, yace babu korafin da aka gabatar musu kawo yanzu.
Shugaban kwamitin Dr Tony Macfoy yace, tun bayan da suka bayyana zuwansu a ranar asabar din data gabata suke zama a sakatariyar Jam’iyyar APC dake Hotoro domin karbar korafin, amma dai har kawo wannan lokaci babu Wanda ya gabato da korafinsa.
A cewarsa hakan na nuni da cewa zaben da akayi a Kano babu korafi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tun daga lokacin zuwan kwamitin a ranar asabar, shugaban kwamitin Dr Tony Macfoy yace korafin zaben da akayi a rufaffen dakin wasa na Sani Abacha zasu karba.
Kwamitin dai na da ragowar kwanaki biyar kafin wa’adin zamansa ya kare.