By Ishaq Dabai
Hukumar Hisbah dake jihar Kano ta jaddada kudurinta ta na ganin ta cafko jaruma Ummah Shehu bisa kalaman data furta ga hukumar.
Hukumar Hisbah ta bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da tayi da Jaridar Dimokuradiyya, ta bakin mai magana da yawun ta Lawal Ibrahim Fagge, inda ya ce, ”Duk randa Allah yasa Ummah ta shigo jihar Kano to lallai zamu neme ta domin ta kare kanta bisa kalaman da ta yi akan hukumar”.
“Koda yake a hukumance bamu fitar da sanarwa cewa muna neman ta ba, amma dai a zahirance akwai wani abu mai kama da haka”.
“Kuma mun yi hakan ne Saboda sha’anin tsaro domin ba komai ne in zaka yi kake fada ba” a cewar sa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tun a farkon wannan sati ne dai Ummah ta fito tana kalubalantar hukumar Hisbah bisa kamun da ta yiwa wata matashiya mai suna Sadiya Haruna da take yada hotunan badala, a kafar sada zumunta, inda kotu ta yanke mata hukuncin komawa Islamiyya.
Wannan dalili yasa Ummah tayi nuni da cewa suma wasu daga cikin jami’an hukumar ta Hisbah sukan taba wannan sha’ani kuma dama hukumar tafi aiki akan yayan talakawa.